Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta yi alƙawarin biyan dukkan bashin ƴan fansho na 2026, zuwa Afrilun 2027.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta yi alƙawarin biyan dukkan bashin ƴan fansho na 2026, zuwa Afrilun 2027.

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin biyan dukkan bashin ƴan fansho na shekarar 2026, zuwa watan Afrilun 2027.

‎Kwamishinan Yaɗa Labarai na jiha, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai bayan kammala zaman Majalisar Zartaswa na musamman da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.

‎Kwamishinan ya ce bashin fanshon ya shafi daga watan Janairun 2019 zuwa shekarar 2026,

Ya kuma bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin biyan dukkan bashin da ya rage tsakanin watan Nuwamban 2026 zuwa Afrilun 2027.

‎Ya ƙara da cewa za a gudanar da biyan kuɗaɗen ne ta hannun hukumar kula da asusun fansho ta jihar Kano, wato Kano State Pension Trustee Board.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM