Koma Labarai
Labarai

SERAP, ta buƙaci Shugaban Najeriya, Tinubu ya bayyana yadda yake rabon tallafin Naira 50,000.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
SERAP, ta buƙaci Shugaban Najeriya, Tinubu ya bayyana yadda yake rabon tallafin Naira 50,000.

Ƙungiyar SERAP mai rajin kare haƙƙin jama’a da tabbatar da adalci a Najeriya, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta bayyana yadda take samun kuɗi da gudanar da shirin tallafin N50,000 ga 'yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi.

Ƙungiyar ta aika da buƙatar bayanai ga ministan harkokin jinƙai da rage talauci, Dokta Bernard Doro, ranar 7 ga Nuwamba, 2026, ta hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare.

A wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, SERAP ta nemi gwamnati ta bayyana adadin kuɗin da aka ware wa shirin, yadda ake zaɓen waɗanda za su amfana da shi, da kuma yadda ake gudanar da biyan kuɗin, kamar yadda kafar DCL Hausa ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM