Kwamitin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da daba ya kama kwayoyin Pregabalin Miliyan 3.18 a Kano.

Kwamitin kar ta kwana da ke yaƙi da miyagun ƙwayoyi da daba a Kano, ya kama mutum ɗaya tare da ƙwato ƙwayoyin maganin Pregabalin da ake zargin na miyagun ƙwayoyi ne kimanin miliyan 3.18 a yankin Sabon Gari da ke Kano.
Kwamitin ya ce ya kama mutumin mai suna Gregory Ogbuji, mai shekaru 34, a wani samame da ta kai wani gida da ke lamba 13, Apple Avenue, Normansland, Sabon Gari, cikin ƙaramar hukumar Fagge.
A wata sanarwa da sakataren kwamitin yaɗa labarai na kwamitin Lamara Garba, ya fitar, ya ce samamen ya biyo bayan samun sahihan bayanan sirri ta hanyar hanyoyin sadarwar kwamitin.
Ya ce kamen ya zo ne ƙasa da sa'o'i 24 bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da rundunar ɗaukar matakin gaggawa domin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.
Sanarwar ta ce an gurfanar da wanda ake zargin bisa sashe na 249 na dokar Penal Code, yayin da wani mutum da ake zargin yana da alaƙa da lamarin ya tsere.
Shugaban Kwamitin, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana nasarar a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin farko da rundunar ta samu, yana mai cewa kusan takwas cikin mutane 10 da ake kama wa a ayyukan yaƙi da miyagun ƙwayoyi na da alaƙa da shan kwayar Pregabalin.
Ya kuma yi kira ga jama'a da su riƙa kai rahoton duk wani motsi da suke zargin yana da alaƙa da fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, yana mai jaddada cewa haɗin kan al'umma na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a jihar Kano.



