Matatar ruwan famfo ta ƙaramar hukumar Tudun Wada a Kano, ta dawo aiki bayan shekaru da dama ba ta aikin.

Matatar ruwan famfo da ke ƙaramar hukumar Tudun Wada a jihar Kano, ta dawo aiki ka'in da na'in bayan kwashe shekaru da dama ba ta aiki.
Yanzu haka da matatar tana samar da tsaftataccen ruwan sha lita miliyan biyu da dubu ɗari a kullum.
Kwamishinan ma'aikatar albarkatun Ruwa na jihar, Dakta Ɗahiru Muhammad Hashim ne, ya bayyana hakan yayin duba matatar a ranar Juma'a 06 ga watan Nuwamba, 2026.
Ya ce gyaran da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranta ya dawo da ruwan sha a unguwannin Gawo, da Tsauni da Tsohuwar NITEL da Unguwar Gabas.
Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa, Dr. Hashim, ya kuma ce ma’aikatar na shirin ƙara ƙarfin matatar zuwa lita miliyan huɗu da dubu ɗari biyar a kullum, domin faɗaɗa isar da ruwa zuwa sauran al’ummomi da ƙauyukan ƙaramar hukumar Tudun Wada a Kano.



