Idan kullum za a rinƙa tura mini kyautar 50,000, ba zan zaɓi Tinubu ba a 2027 - Buhari Yunusa Kumurya

Ɗan gwagwarmayar nan a Najeriya, Kwamared Buhari Yunusa Kumurya, ya yi rantsuwar cewa Wallahi idan a kullum za a rinƙa tura masa tallafin Naira dubu 50,000, ba zai zaɓi shugaban ƙasa Bola Tinubu ba, a zaɓen 2027.
Kwamared Buhari Yunusa Kumurya ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook, a ranar Alhamis 05 ga watan Nuwamba, 2027.
Buhari Kumurya ya ce shima an tura masa tallafin naira dubu 50,000, daga Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
A cewar sa, ya rantse da Allah, idan kullum za a masa Naira 50,000, daga nan har zuwa ranar zaɓe, ba zai zaɓi Tinubu ba, domin ya san tsantsar yaudara ce.
A cikin makon nan ne dai ƴan Najeriya, suka fara samun tallafin naira dubu hamsin daga Gwamnatin tarayya, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.



