Rikici: A gaggauta shiga tsakanin Fulani da Manoma a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa - Human Right

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakin daƙile cinnawa gonakin mutane wuta, da dukan da ake zargin wasu Fulani na yi wa wasu manoma a wasu yankuna na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Ko-odinatan Ƙungiyar na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Kwamared Yusuf Garba, ne ya bayyana hakan ga Dala FM Kano, a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba, 2026.
Yusuf Garba ya bayyana cewa, ko a cikin makon nan sai da wasu Fulani da suka je wucewa da Shanu aka yi zargin sun cinna wuta a gonar wani mutum, saboda ya hana shanun su shigar masa gona.
A cewar sa, "An kuma zargi fulanin sun daki wani mutum mai suna Mallam Abdulsalamu Lawan, saboda ya yi wa mai kora shanun maganar cewar ka da ya kora masa shanu acikin gonar sa, in ji shi.
Kwamared Yusuf ya ce unguwannin da lamarin ya shafa sun haɗar da Unguwar Gwanje, zuwa Ci Goro, labun Hago, da Ɗan guguwa daura da Gabari, da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, a Kano.
A cewar sa, "Duk shekara lokaci irin wannan na Kaka, manoman yankunan sukan fuskanci wannan matsalar, wanda idan fulanin suka je wucewa suke takurawa manoma irin hakan," in ji Yusuf.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da shugabancin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, da dukkanin masu ruwa da tsaki, da su gaggauta shiga tsakanin manoma da fulanin domin daƙile wannan matsalar a tsakanin su.
A cewar sa, matuƙar za a ɗauki matakan da suka dace babu makawa za a daƙile faruwar rikici a tsakanin manoma da Fulani, kasancewar zaman lafiya ya fi komai daɗi.



