Ƙungiyar matasan ƴan jarida ta gudanar da taron wayar da kan ɗalibai kan illar shaye-shaye a Kano.

Ƙungiyar matasan ƴan jarida ta jihar Kano, wato Kano Youth Journalist Forum, ta gudanar da taron wayar da kan ɗaliba makarantar sakandaren maza ta G.S.S Gwale, a kan illolin ta'ammali da kayan shaye-shaye.
Ƙungiyar ta gudanar da taron ne a ɗakin taro na Makarantar Sakandiren maza ta G.S.S Gwale, a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba, 2026.
Taron ya samu halartar wakilai daga ma'aikatar ilimi ta jihar Kano, da hukumar Shari'a ta jihar Kano, Hukumar NDLEA, wakilan gwamnatin Kano, hukumomi da ma'aikatu, da ɗaliban makarantar sakandaren maza ta G.S.S. Gwale, da dama.
Da yake yi wa gidan rediyon Dala FM ƙarin bayani, Shugaban ƙungiyar matasan ƴan jarida ta jihar Kano, Kwamared Musa Zangina Adam, ya ce sun shirya taron wayar da kan ɗaliban ne a makarantun gwamnati na Sakandiren maza da mata guda biyar, domin wayar da kan ɗalibai illar ta'ammali da kayan maye.
A yayin taron, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, na daga cikin waɗanda suka gabatar da maƙala a kan illar ta'ammali da kayan maye a mahanga ta addinin Musulunci.
Sheikh Ɗanabba ya ce abinda ƙungiyar ta yi abun a yaba ne, duba da yadda wasu daga cikin matasa a jihar Kano, ke fuskantar ƙalubale na ta'ammali da kayan maye, yana mai cewa akwai buƙatar kowa ya sanya hannu wajen ganin an daƙile wannan matsalar.
Da yake nasa jawabin, Mataimakin Babban Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, da ke kula da sashen wayar da kan al'umma da kuma riga-kafi a kan haɗarin miyagun shaye-shaye, ACN Muhammad M Alƙali, ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar kan taron wayar da kan matasan da ta shirya a kan illar ta'ammali da kayan maye.
A nasa ɓangaren, Shugaban zauren Majalisar ƙoli na malamai, na ƙasa reshen jihar Kano, Mallam Ibrahim Khalil, ya ce fara daƙile abinda ya sa matasa suke shaye-shayen kayan maye, na taka rawa wajen daƙile matsalar.
Abubakar Mu'azu Mojo shi ne shugaban ƙaramar hukumar Gwale, ya ce abunda ƙungiyar matasan ƴan jaridar ta jihar Kano, ta yi, abu ke da ke taimaka wa gwamnati da al'umma, inda ya ce ƙaramar hukumar ta duƙufa wajen ƙara daƙile wannan matsala ta shaye-shaye.
Taron wayar da kan ya samu halartar al'umma da dama, kuma ciki har da wakilci daga Ma'aikatar ilimi ta jihar Kano, da Shugabannin makarantar sakandaren maza ta G.S.S Gwale, da tsohon shugaban ƙungiyar dattawan arewa ACF, reshen jihar Kano, Gwani Umar Farouk, da Ƙungiyar ɗaliban makarantar Sakandaren maza ta G.S.S Gwale, da jami'an tsaro da sauransu.



