Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta tantance tare da amincewa gwamnan Kano, ya naɗa Sanusi Bature kwamishina

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta tantance tare da amincewa gwamnan Kano, ya naɗa Sanusi Bature kwamishina

Majalisar dokokin ta tantance tare da amincewa gwamnan Kano ya naɗa tsohon mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Ahmad Bature, bayan shafe tsawon sama da rabin sa a a gaban majalisar.

Bayan kammala tantance shi, Bature ya ce zai farfaɗo da gidan jaridar Triumph da sauran kafafen yaɗa labaran Gwamnati.

Ya kuma ce zai taimaka wa kafafen yaɗa labarai masu zaman kan su domim ɗorewa.

Kazalika majalisar ta tantance tsohon Kakakin majalisar a lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, Balarabe Sa'idu Gani.

Balarabe Gani ya bayyana jin daɗin sa tare da cewa zai taimaki Gwamnati wajen samar da ayyukan cigaba a jihar Kano.

Wakilinmu na majalisar Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, majalisar ta kuma naɗa Sule Lawan Shuwaki na jam'iyyar PDP, a matsayin mataimakin bulaliyar majalisar na marasa rinjaye.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM