Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta samar da kamfanin sarrafa kayan aikin gona a Ɓagwai da Shanono.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Majalisar dokokin Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta samar da kamfanin sarrafa kayan amfanin gona a ƙananan hukumomin Ɓagwai da kuma Shanono, da ke jihar.
A zaman majalisar na yau Litinin, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore, ɗan majalisar Ɓagwai da Shanono, Ali Lawan Alhassan Kiyawa ne ya gabatar da ƙudirin hakan a gaban zauren majalisar.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano, Sanusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, Ali Lawan Kiyawa, ya ce samar da kamfanin zai taimaka wajen rage asarar da manoma ke yi a wannan musamman la'akari da yadda suka shahara da noman Tumatur da Shinkafa.



