Hisbah ta kama Ishaku Musa, bisa zargin sayar da naman kare da giyar burukutu a Kano.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wani mutum mai suna Ishaku Musa, mazaunin unguwar Sharaɗa Phase 3, layin Aliko, bisa zargin sayar da naman kare da giyar burukutu.
Wannan na cikin sanarwar da Kwamandan Hisbah na Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Hamidan Tanko Alasaka, ya fitar a ranar Lahadi, 01 ga Nuwamba, 2026.
Kwamandan ya ce, jami’an hukumar sun bi diddigin wanda ake zargin tun daga wajen da ake zargin ya ɗauko naman a unguwar Sabon Gari, inda ya nufi kai shi Panshekara.
Sanarwar ta bayyana cewa wanda ake zargin yana hannun hukumar, inda ake ci gaba da bincike a kan sa, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.
Kwamandan ya kuma shawarci jama’a da su rinƙa kai bayanai kan duk wanda suke zargin yana sayar da naman da ba su gamsu da ingancinsa ba.



