Ɗaliban Marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, sun makusanta cewar ƙungiyar Ansaruddin ce ta kashe malamin.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Ɗaya daga cikin mabiyan malamin, Nazifi Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da wakilinmu Nura Bello.
Nazifi ya ce suna jiran mahukunta su gudanar da cikakken bincike tare da bayyana waɗanda suka kashe malamin, maimakon dogaro da ikirarin da ƙungiyar ta yi.
Ya jaddada cewa ya kamata a bar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.



