Koma Labarai
Labarai

Majalisar dokokin Kano ta gyara tare da rage kasafin kuɗin jihar saboda sabuwar dokar haraji.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisar dokokin Kano ta gyara tare da rage kasafin kuɗin jihar saboda sabuwar dokar haraji.

Majalisar dokokin Kano ta gyara tare da rage kasafin kuɗin jihar Kano, sakamakon sabuwar dokar haraji ta ƙasa.

Majalisar tayi gyaran dokar kasafin 2026 ne a zaman ta na yau Talata, bayan da Gwamnan Kano ya nemi a sake dubawa tare da gyara dokar.

Tun da fari kasafin kuɗin jihar a farkon shekarar 2026 ya kai Tiriliyan Ɗaya da Biliyan Ɗari huɗu da Arba'in da Bakwai, inda ya nemi a dawo da shi kasa zuwa Tiriliyan Ɗaya da Biliyan Ɗari Biyu da Ashirin da biyu.

Haka kuma a zaman majalisar na wannan rana ta amince da gyaran dokar kafa ƴan sandan jihohi.

Lawan Husaini Ceɗiyar ƴan gurasa, shugaban masu rinjaye na majalisar, ya bayyana irin gyare-gyaren da aka yiwa dokokin biyu.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM