Koma Labarai
Labarai

Ƴan Najeriya na kashe har kashi 120 na kuɗin shigarsu wajen siyan Abinci – Ministan Tinubu

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan Najeriya na kashe har kashi 120 na kuɗin shigarsu wajen siyan Abinci – Ministan Tinubu

Ministan kuɗi kuma mai kula da yattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa wasu ƴan Nijeriya na kashe kuɗin da ya kai kashi 120 cikin 100 na kuɗin shigarsu wajen sayen abinci a ƙasar.

Ministan ya ce lamarin ya tilasta wa mutanen karɓar bashi ko dogaro da ƴan uwansu domin rayuwarsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Oyedele ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan.

Ya ce wani binciken da gwamnati ta gudanar ya nuna cewa, kuɗin da wasu iyalai ke kashewa wajen sayen abinci ya zarce kuɗin shigarsu.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM