Koma Labarai
Labarai

Majalisar dokokin Kano ta amince da naɗin sabbin kwamishinoni shida da gwamna ya aike mata

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisar dokokin Kano ta amince da naɗin sabbin kwamishinoni shida da gwamna ya aike mata

Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da naɗin sabbin kwamishinoni shida da Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya aika mata, domin tantancewa da amincewa.

Waɗanda aka tabbatar sun haɗa da tsohon Air Commodore Salisu Yusha’u, Hon. Ibrahim Namadi, Farfesa Sani Lawan, Hon. Muktar Ishaq Yakasai, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa da Hon. Idris Garba Mustapha.

An gudanar da tantancewar ne a zaman majalisar na ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore.

A yayin zaman, kakakin ya sanar da ‘yan majalisar sunayen waɗanda gwamnan jihar ya miƙa domin tantancewa da tabbatar da naɗinsu.

Bayan kowanne ya gabatar da kansa a gaban majalisar, ‘yan majalisar sun bayyana gamsuwarsu da ƙwarewarsu, cancantarsu da gogewarsu wajen gudanar da ayyukan da aka naɗa su domin yi.

Sanarwar da sakataren yaɗa labarai na majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar ta bayyana cewa ‘yan majalisar sun yi la’akari da dacewar naɗin waɗanda aka zaɓa a wannan lokaci da ake buƙatar gudummawarsu wajen ci gaban jihar.

Daga cikin ‘yan majalisar da suka ba da gudummawa yayin tattaunawar akwai wakilan Doguwa, Tudun Wada, Fagge, Kiru, Madobi, Dala da Aliyu Bagwai/Shanono.

A ƙarshen tantancewar, majalisar ta amince da dukkan sunayen kwamishinonin shida, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan amincewa ta share fage ga matakin da gwamnan zai ɗauka na tura su ma’aikatu ko sassan da za su jagoranta a gwamnatin jihar Kano.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM