Koma Labarai
Labarai

An ƙirƙiri labarin kai wa tawagar Kwankwaso hari a Bichi ne don neman tausayawar jama’a – Gwamnatin Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An ƙirƙiri labarin kai wa tawagar Kwankwaso hari a Bichi ne don neman tausayawar jama’a – Gwamnatin Kano

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi tafiyar Kwankwasiyya da ƙirƙirar labarin kai wa magoya bayanta hari a ƙaramar hukumar Bichi, domin neman tausayin jama’a.

Sanusi Bature ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba, 2026.

Sanusi Bature ya kuma nuna shakku kan rahoton harin saboda rashin hotuna ko bidiyoyin da za su tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai a wani rahoto, Jaridar Daily Trust ta fitar ta ce, wasu ’yan daba da ake zargi sun kai hari kan ayarin motocin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, yayin ziyarar yaƙin neman zaɓe a Bichi, a ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamba, 2026.

Tuni dai ɗan takarar shugaban ƙasa a NDC Peter Obi, ya nemi jami'an ƴan sanda, da hukumomin tsaro su gaggauta bincike kan harin da aka kai wa ayarin motocin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a Karamar Hukumar Bichi.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM