Koma Labarai
Labarai

Ƴar Kwankwaso ta buƙaci Gwamnan Kano ya saketa ta hanyar kul'i a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴar Kwankwaso ta buƙaci Gwamnan Kano ya saketa ta hanyar kul'i a Kano.

Matar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wato Zainab Rabi'u Musa Kwankwaso, ta shigar da ƙarar neman a raba aurensu a wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Gudu, Abuja.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa Zainab, wadda ’yar tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce, ta nemi a raba auren ta hanyar Khul’i, wato tsarin da mace ke neman saki ta hanyar mayar da sadakin da aka biya.

Takardar sammacin kotun mai lamba CV/97/26 ta umarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gurfana a gabanta a ranar 17 ga Nuwamba, 2026.

Zainab ta bayyana a cikin ƙarar cewa ta auri gwamnan ne a ranar 29 ga Yuli, 2006, kuma sun haifi ’ya’ya shida tare.

A cewar takardun ƙarar, ta ce aurensu ya shiga mawuyacin hali sakamakon rashin kulawa, soyayya da kusanci a tsakaninsu, lamarin da ta ce ya sa ta rasa sha’awar ci gaba da zamantakewar auren.

Ta kuma bayyana cewa ƙoƙarin da aka yi na sasanta tsakaninsu bai haifar da sakamako ba, tare da bayyana shirinta na mayar da sadakin da aka biya a lokacin aurensu domin samun damar raba auren.

Rahoton ya ce wannan mataki na zuwa ne bayan samun saɓani tsakanin gwamnan da tsohon ubangidansa na siyasa, kuma mahaifin matar tasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Haka kuma, jaridar ta rawaito cewa Zainab ta bar gidan gwamnatin Kano a ranar 28 ga Oktoba, inda ta koma gidan mahaifinta kafin daga bisani ta tafi Abuja.

Jaridar Daily Nigerian ta ce ta tura saƙonni tare da kiran Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Sanusi Dawakin Tofa, domin jin ta bakin gwamnatin jihar, amma bai mayar da martani ba har zuwa lokacin wallafa rahoton.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM