Gwamnati da iyaye a ƙara jan matasa a jiki don kawar musu da shan kayan maye - Peace Unity and Progres

Ƙungiyar nan da ke rajin samar da zaman lafiya da haɗin tare da yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi ta Peace Unity and Progres, ta buƙaci gwamnatin Kano da iyaye kan su ƙara ruɓanya ƙoƙarin su don ganin an magance shan miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa.
Mataimakin Babban Kwamandan Ƙungiyar mai kula da yankin Kano ta Kudu, ACU Salisu Gambo, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamba, 2026.
ACU Salisu Gambo ya ce matuƙar gwamnatin jihar Kano, da iyaye da sauran al'umma, za su ƙara jan matasa a jiki, tare da nema musu sana'o'i, babu makawa za a cire musu munanan daɓi'u.
A cewar sa, suma a nasu ɓangaren yanzu haka shirin su ya yi nisa wajen jan matasa a jiki, ciki har da ɗaliban makarantun tsangaya da na boko, kuma asibitoci domin tallafa jama'a ta bangarori daban-daban, don magance matsalolin da ake fuskanta tare da rage musu wani raɗaɗi.
Ya ce yanzu haka ƙungiyar su ta shirya tsaf wajen shirya wa ɗaliban makarantun sakandare da na tsangayu taron wayar da kai kan illar ta'ammali da kayan maye.
A ƙarshe, Ƙungiyar ta Peace Unity and Progress ta ƙasa reshen jihar Kano, ta kuma buƙaci matasa da su gujewa shiga harkokin daba, shan kayan maye da kuma ƙwacen waya, domin ganin goben su ta yi kyau.



