Daraktan Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, na Kano, Alhaji Sule Aliyu ya rasu.

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta ƙasa, ta bayyana rasuwar Daraktan ta na jihar Kano, Alhaji Sule Aliyu, sakamakon gajeriyar rashin lafiya.
Babban Daraktan Ƙungiyar a Najeriya, wanda yanzu haka ke ƙasar Qatar, Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a cikin daren ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba, 2026.
Ya ce Daraktan Ƙungiyar, ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba, 2026, a asibiti, bayan da aka kwantar da shi a ranar Talata 10 ga watan Nuwamban 2026, bisa rashin lafiyar da ta kama shi.
Sanarwar ta ce za a yi jana'izar Marigayin a gidan sa da ke Ƙofar Naslsarawa, bayan Badala, da misalin ƙarfe 08:00 na safiyar gobe Alhamis 12 ga watan Nuwamba, 2026.
Ambasada Ƙaribu Yahaya Lawan Kabara, ya bayyana Marigayi Alhaji Sule Aliyu a matsayin mutumin kirki, mai kula da ibada da kuma ƙoƙari wajen rajin kare haƙƙin bil'adama, da samar da ci gaba ga al'ummar ƙasar nan.
Ƙaribu Kabara ya kuma yi addu'ar Allah ya jiƙan Marigayin ya sa mutuwa ta zama hutu a gare shi, ya albarkaci abinda ya bari, da sauran al'ummar Musulmi baki ɗaya.



