Kotu ta baiwa KCPC umarnin ƙona Garin Alƙama sama da buhu 400, da ta kama a Kano.

Kotun da ta saurari wata ƙara da Hukumar KCPC ta kai mata bayan kama wani garin Alkama da ya lalace, kimanin buhu ɗari huɗu da ɗoriya, ta bayar da umarnin ƙona garin ko lalata su, domin gudun kada su sake komawa ga al’umma.
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da Kai na Hukumar KCPC, Jamilu Mustapha Yakasai, ya fitar a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba, 2026.
Sanarwar ta ce Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta samu nasarar kama kayan ne, bayan wani rahoto da ya zo mata a kwanakin baya cewa, an tara buhunan garin Alkama masu tarin yawa da niyyar sayarwa ga al’umma.
Shi ma da yake ƙarin haske kan lamarin, Sakataren Zartarwa na Hukumar, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ya ce hukumar na gudanar da aikinta ne bisa doka da oda, ta hanyar gurfanar da duk wani ɗan kasuwa da ya karya dokokin, yana mai cewa hakan shi ne zai kare lafiyar al’ummar Jihar Kano.
Dr. Ibrahim Garba ya kuma jaddada buƙatar da ke akwai ga ’yan kasuwa, da su ba wa hukumar haɗin kai, inda ya ce hukumar ba ta da niyyar cusgunawa kowa, sai dai ƙoƙarin ɗora kowa bisa ƙa’ida wajen sayar wa mai saye kaya ba tare da an zakince shi ba.
Sakataren Zartarwar ya kuma gode wa al’umma bisa yadda suke ƙara fahimtar KCPC da irin ayyukanta, sannan ya ƙara ƙarfafa musu gwiwa kan su riƙa kula da dukkanin kayayyakin da za su saya kafin su kulla duk wani ciniki.
A ƙarshe, ya gode wa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa irin haɗin kan da yake bai wa hukumar ba dare ba rana, inda ya bayyana hakan a matsayin nasara ga ayyukanta.



