Koma Labarai
Labarai

Kamfanin Air Peace ya sauke fasinja daga jirgi bayan ya ce fushinsa zai iya ƙona jirgin.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kamfanin Air Peace ya sauke fasinja daga jirgi bayan ya ce fushinsa zai iya ƙona jirgin.

Rahotanni sun bayyana cewa, Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya sauke wani fasinja daga cikin jirginsa bayan ya yi cacar baki da ma’aikatan jirgin, tare da cewa fushin da yake ciki zai iya ƙona jirgin baki ɗaya.

Hukumar kula da sufurin Jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ce ta bayyana hakan, inda ta ce lamarin ya jawo jinkirin tashin jirgin bayan da matuƙin jirgin ya umarci a mayar da shi wurin ajiye jirage.

Daraktan hulɗa da jama’a da kare haƙƙin masu amfani da hukumar, Michael Achimugu, ya ce lamarin ya faru ne a jirgin Air Peace mai lamba P47866 da ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Asaba da ke Jihar Delta.

Kafar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin, Achimugu ya ce fasinjan mai suna Celestine Ezeudu ya ƙi bin umarnin ma’aikatan jirgin na dakatar da ɗaukar hotuna da kuma ajiye wayarsa yayin da jirgin ke shirin tashi.

Ya ka ce bayan wani ma’aikacin jirgin ya sake tunkararsa domin umartar sa da ya bi ƙa’ida, sai aka samu saɓani a tsakaninsu.

A yayin cacar bakin ne fasinjan ya ce: “Fushin da nake ji zai iya ƙona wannan jirgin.”in ji shi.

Sanarwar ta ce ma’aikatan jirgin sun sanar da matuƙin jirgin nan take, wanda ya bayar da umarnin mayar da jirgin wurin ajiye jirage da misalin ƙarfe 3:57 na yamma.

Kazalika, Achimugu ya ce daga bisani fasinjan ya amince da umarnin saukarsa daga jirgin ba tare da wani ƙarin turjiya ba.

Ya ƙara da cewa abokinsa da suke tafiya tare shi ma ya sauka da kansa domin nuna goyon baya gare shi.

A cewar jami’in, lokacin da aka yi wa Ezeudu tambayoyi, ya bayyana cewa fushinsa ya samo asali ne daga rashin samun damar shiga wani jirgin da ya kamata ya fara tafiya da shi.

Sai dai ya ce fasinjan bai yi tsammanin halayensa za su sa a mayar da jirgin da ya shiga wurin ajiye jirage ba gaba ɗaya.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM