Majalisa ta gargaɗi kwamishinan yaɗa labaran Kano, da ya dai na fitar da sanarwar da ta shafe ta.

Majalisar dokokin jihar Kano ta gargaɗi kwamishinan yaɗa labarai na jihar, da ya dai na fitar da kowace irin sanarwa da ta shafi majalisar.
A zaman majalisar na ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba , 2026, shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Husaini Dala ne ya bayyana irin hakan.
Lawan Hussaini ya ce, kwamishinan yana fita da labarin da ya shafi majalisar tun kafin ya zo gabanta, wanda yin hakan kuskure ne.
Shugaban masu rinjayen ya ce, doka ta bawa gwamna damar gabatar da kasafin kuɗin a gabanta, kafin daga bisani ta amince masa tare da bashi damar gabatar mata a lokacin da ta bashi.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sunusi Shuaib Musa ya ruwaito cewa, majalisar ta karɓi wasikar gwamnan tare da amincewa ya gabatar da kasafin a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba 2026.



