Jarin ƴan kasuwa 40 ne ya karye saboda lalacewar titin Kuntau a Kano - Ƴan kasuwa

Ƙungiyar ƴan kasuwa a unguwar Kuntau da kewaye, da ke ƙaramar hukumar Gwale, sun buƙaci gwamnatin Kano ta bada umarnin ci gaba da aikin titin da ya taso daga bayan tashar Rijiyar Zaki ya biyo ta yankin su ya haɗe da Titin Madobi.
Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Kabiru Ali Abubakar Gwarzo, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano.
Ya ce a baya gwamnatin Kano ta fara gudanar da aikin gyaran titin amma kawo yanzu aikin ya tsaya cak, sun kuma yi bakin ƙoƙarin su domin ganin an ci gaba da aikin amma kawo yanzu shiru.
A cewar sa, "Yanzu haka kusan ƴan kasuwar mu 40, ne jarin su ya karye sakamakon lalacewar titin, bisa yadda Ƙura take turnuƙe su lamarin da ya haifar musu da rashin ciniki a kasuwancin su," in ji Kabiru.
A nasa ɓangaren, limamin masallacin juma'a na Kwanar Kuntau, Mallam Baƙir Kabir Khalil Ƙofar Ƙwaru, ya ce hanyar ta haura shekaru 15 tana damun su bisa lalacewar da ta yi.
A cewar sa, suna matukar shan wahala wajen zirga-zirga a hanyar, musamman ma a lokacin damuna, da hanyar ke zama alaƙaƙai a gare su bisa gwajab-gwajab da masu ababen hawa suke fuskanta.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta kai musu ɗauki wajen kammala aikin titin yankin nasu domin ganin sun samu wani sauƙi.
Mazauna yankin Kuntau da kewayen dai sun yi fatan za a kai musu ɗauki wajen ƙarasa gyaran titin domin sauƙaƙa wa al'umma.



