Koma Labarai
Labarai

Gwamnan Kano ya kamata a gaggauta sanya hannu a hukuncin kisan Umar da Yakubu - Human Right

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Kano ya kamata a gaggauta  sanya hannu a hukuncin kisan Umar da Yakubu - Human Right

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Right and charity development initiative, ta yi kira ga Gwamnan Kano Abba Kabir, da ya gaggauta sanya hannu domin zartas da hukuncin kisan da kotu ta yi wa Umar da Yakubu, bisa samun su da laifin kashe uwa da ƴaƴanta 6 a unguwar Ciranchi Ɗorayi.

Babban Daraktan Ƙungiyar a Najeriya, Kwamared Auwal Jibril Maifada ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano, ranar Lahadi 8 ga watan Nuwamba, 2026.

A ranar juma'a 6 ga watan Nuwamba, 2026, ne dai Babbar Kotun jihar Kano, mai lamba 11, da ke zaman ta a Bompai, ta yanke wa Umar Auwalu da Yakubu Ɗayyabu, hukuncin kisa ta hanyar rataya, da ɗaurin rai da rai.

Kotun ta yanke musu hukuncin ne bayan da ta same su da laifin kashe wata matar aure mai suna Fatima Abubakar da ƴaƴanta 6 a unguwar Chiranchi da ke yankin Ɗorayi, a Kano.

Sai dai kotun ta wanke Isyaku Yakubu, wanda akafi sani da Cobe, bisa rashin samun sa da laifi a kisan gillar.

Babban Daraktan Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin, Kwamared Auwal Maifada, ya ce akwai buƙatar Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a hukuncin kisan, matuƙar lokaci ya ƙure matasan ba su ɗaukaka ƙara ba.

A cewar sa, rashin imanin da matasan suka aikatawa iyalan Mallam Bashir Haruna, bai kamata a ɗaga musu ƙafa ba, yana da kyau a zartar musu da hukuncin domin zama izinina ga sauran mutane.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM