Koma Labarai
Labarai

Takarar Atiku Abubakar tana nan duk da hukuncin kotu - Lauya

Hassan Mamuda Ya'u 15 views
Takarar Atiku Abubakar tana nan duk da hukuncin kotu - Lauya

Lauyan nan mai zaman kansa Barista Lawan Lawan Usman, ya ce hukuncin babbar kotun tarayya bai rushe takarar Atiku Abubakar ba, har sai idan ya kai sati biyu bai ɗaukaka ƙara ba.

Lauyan ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron dinki ta cikin shirin Jamhuriya na Dala FM Kano, da ya gudana a cikin daren ranar Alhamis 05 ga watan Nuwamba, 2026.

A jiyan ne dai Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta soke sahihancin shugabancin David Mark a jam’iyyar ADC, tare da bayyana cewa matakan da kwamitin riƙon ƙwaryar ya ɗauka ba su da inganci,

Hukuncin dai ya nuna cewa ciki har da tsayar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.

Sai dai Barista Lawan Lawan ya ce, hukuncin bai shafi takarar Atiku Abubakar ba, musamman ma idan jam'iyyar ta ɗaukaka ƙara, daga nan shima hukuncin ya tsaya har sai kotun sama ta yi hukunci.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM