Koma Labarai
Labarai

Hukumar KCPC ta kama lemukan da wa'adin su ya ƙare fiye da guda 5,500, a kasuwar Singa, Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar KCPC ta kama lemukan da wa'adin su ya ƙare fiye da guda 5,500, a kasuwar Singa, Kano.

Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Jihar Kano (KCPC) ta kama wani lemo da wadinsa ya kare kuma ake kokarin siyarwa da al'umma shi a kasuwa.

Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da Kai na Hukumar ta (KCPC), Jamilu Mustapha Yakasai, ya fitar a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba, 2026.

Sanarwar ta ce lamarin ya biyo bayan wani rahoto da hukumar ta samu, na cewa wani ɗan kasuwar ya tara lemun Roba da wa'adin amfaninsu ya ƙare.

Hukumar ta ce bisa wannan rahoto ne ta gaggauta tura jami'anta kasuwar domin tabbatar da cewa kayayyakin ba su shiga hannun al'umma ba.

Hukumar ta kara da cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikinta ba tare da nuna sani ko sabo ba.

Haka kuma, ta tabbatar wa al'umma cewa za ta ci gaba da bin diddigin irin waɗannan kayayaki, domin kare haƙƙin mai saye a fadin jahar Kano.

Da yake ƙarin haske kan lamarin, Daraktan da ke kula da sashen samame da kawar da gurbatattun kayayyaki na hukumar, Alhaji Auwalu A. Muhammad, ya bayyana cewa hukumar na gudanar da aiki bisa doka da oda wajen ganin dukkanin kayan da wa'adinsu ya kare ko a canja muhimman Bayanai dake jikin mazubi ko makamancin hakan.

Hukumar ta kuma ce a shirye take ta kwace domin kawar da shi daga kasuwa.

Shima da ya ke karin Haske kan lamarin Sakataren Zartarwa na hukumar, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ya sake jaddada aniyar hukumar na ci gaba da kai samame a kasuwanni, rumfunan kasuwanci da manyan shaguna domin kawar da kayayyakin da suka lalace ko wa'adin amfaninsu ya ƙare.

Ya ci gaba da cewa hukumar ba za ta lamunci cin zarafi ko wulaƙanta jami'anta ba, yana mai cewa jami'an suna gudanar da aikinsu ne domin kare lafiyar al'ummar Jihar Kano daga cututtukan da ka iya biyo bayan amfani da gurbatattun kayayyaki.

Dr. Ibrahim ya kuma yi kira ga 'yan kasuwa da su mara wa ƙoƙarin hukumar baya ta hanyar taimakawa wajen gano da kuma cire duk wani kaya da ya lalace, maimakon ɓoyewa ko sauya masa wa'adin amfani, ya ce yin hakan zai taimaka wajen kare lafiyar masu sayayya da kuma bunƙasa kasuwancinsu.

A ƙarshe, ya yabawa Gwamna Engr Abba kabir yusuf bisa dama da shalewa da yake bawa hukumar domin ta gudanar da aikin ta

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM