Koma Labarai
Labarai

Hukumar Shari'a ta Kano, ta sha alwashin ɗaukar mataki kan masu haɗa bidiyon Ruƙumin AI, da ke ɗura ashar.

Hassan Mamuda Ya'u 2 views
Hukumar Shari'a ta Kano, ta sha alwashin ɗaukar mataki kan masu haɗa bidiyon Ruƙumin AI, da ke ɗura ashar.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta ce ta duƙufa wajen neman wanda yake haɗa bidiyon Raƙumin AI, wanda yake ɗura ashar ake ɗorawa a shafukan sada zumunta, domin ɗaukar mataki a kan sa.

Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba ne ya yi wannan barazanar a zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Malamin ya ce suna ta neman wanda yake amfani da Raƙumin musamman in a Jihar Kano ne, yana mai kira a gare shi da ya tubarwa Allah, sannan ya cire abubuwan da ya sa a Kafafen sada Zumunta, duba da yadda hakan ke ɓata tarbiyyar al'umma.

Ya kuma buƙaci duk waɗanda ke haɗa bidiyon Ruƙumin AI, da ke ɗura ashar da su ji tsoron Allah, su daina, domin gujewa fushin hukumar, yana mai cewa ba za su zuba ido su bari wannan abu ya ci gaba da faruwa ba.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM