Koma Labarai
Labarai

Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙudurori fiye da Sittin da ɗaya a shekarar 2026.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙudurori fiye da Sittin da ɗaya a shekarar 2026.

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta amince da ƙudurori fiye da Sittin da ɗaya a shekarar 2026.

A zaman majalisar na yau, Jibril Ismail Falgore ne ya bayyana hakan, bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar mata da kasafin kuɗin shekarar 2027.

Kasafin kuɗin da Gwamnan ya gabatar a yau Laraba, ya kai Tiriliyan ɗaya da Biliyan 107, inda ɓangaren ilimi ke da mafi rinjaye da kaso 30 sai kuma Lafiya dake da kaso 15 yayin da ababen more rayuwa ke da kaso 20.

Falgore ya kuma ce za su yi ƙoƙarin ganin sun kammala aikin kasafin kuɗin na baɗi domin cigaba da ayyukan da Gwamnan ke yi.

Wakilinmu na majalisar Sunusi Shuaib Musa ya ruwaito cewa, kakakin majalisar ya raka gwamnan don duba aikin ginin majalisar da ake cigaba da yi.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM