Koma Labarai
Labarai

Gwamnan Kano Abba Kabir ya gabatar da sama da naira Tiriliyan ɗaya a matsayin kasafin kuɗin 2027.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Kano Abba Kabir ya gabatar da sama da naira Tiriliyan ɗaya a matsayin kasafin kuɗin 2027.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kudirin kasafin kudin 2027, na sama da naira tiriliyan ɗaya da digo ɗaya, a gaban majalisar dokokin jihar a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba, 2026.

Gwamnan ya mika wannan daftari ne a yayin wani zama na musamman da majalisar ta gudanar a babban zaurenta da ke birnin Kano, a gaban shugaban majalisar Jibril Isma'il Falgore, da sauran 'yan majalisar dokokin jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa wannan kasafin kudi mai cike da tarihi an tsara shi ne domin inganta fannonin ilimi, lafiya, da ayyukan raya birane da karkara, tare da bunkasa aikin gona da kuma samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa da mata.

A jawabinsa a gaban majalisar, gwamnan ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da cewa, an aiwatar da kasafin yadda ya kamata domin ci gaba da kawo sauyi a rayuwar al'ummar jihar Kano, tare da cika alƙawuran da gwamnatinsa ta ɗauka.

Gwamna Yusuf ya bukaci yan majalisar da su hanzarta duba wannan kudiri tare da zartar da shi a kan lokaci, domin bai wa gwamnati damar fara ayyukan ci gaba, ba tare da ɓata lokaci ba daga farkon sabuwar shekarar.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM