Koma Labarai
Labarai

Zamu zauna da ƴan siyasar da ke aibata ƴan uwan su a shafukan sada zumunta a Kano - Hukumar Shari'a

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Zamu zauna da ƴan siyasar da ke aibata ƴan uwan su a shafukan sada zumunta a Kano - Hukumar Shari'a

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta jaddada aniyarta na ɗaukar matakin da ya dace a kan duk masallacin da ya rufe hanya yayin sallar juma'a, kasancewar yin hakan ya saɓawa doka.

Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'ar, Sheikh Ali Ɗanabba ne ya bayyana hakan lokacin da yake ƙarin bayani dangane da taron majalisar zartarwa da hukumar ta gudanar, wadda ta samu wakilcin ofishin Sakataren gwamnatin Kano, da hukumar Hisbah da hukumar Zakka.

Taro majalisar zartarwar ya gudana ne a hukumar Shari'ar ta jihar Kano, ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba, 2026.

Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma ƙara da cewa, a yayin taron an tattauna abubuwan da za su ciyar da al'ummar jihar Kano gaba.

Ya kuma ce majalisar zartarwar ta amince da zama da ɓangarorin al'umma, ciki har da ƴan siyasar da ke aibata ƴan uwan su a shafukan sada zumunta, da kalaman da ba su dace ba, domin daƙile matsalar.

A cewar sa, fatan hukumar shi ne a samu ci gaban da ya dace tare da gyaran tarbiyyar al'umma a faɗin jihar Kano.

A ƙarshe, Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma buƙaci al'umma da su ƙara tashi tsaye wajen yin abinda ya kamace su domin ganin goben su ta yi kyau.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM