Koma Labarai
Labarai

Ƙungiyar Matasan ƴan jarida ta gudanar da taron wayar da kan ɗalibai kan illar shan miyagun ƙwayoyi a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƙungiyar Matasan ƴan jarida ta gudanar da taron wayar da kan ɗalibai kan illar shan miyagun ƙwayoyi a Kano.

Ƙungiyar Matasan ƴan jarida ta jihar Kano, ta gudanar da taron wayar da kan ɗalibai a makarantar sakandaren maza ta G.S.S Kawaji da ke ƙaramar hukumar Nasarawa, a kan illar ta'ammali da kayan maye.

Makarantar dai itace ta biyu da ƙungiyar ƴan jaridar ta gudanar da taron wayar da kan ɗaliban daga cikin makarantu biyar da za ta yi a faɗin jihar Kano, a wani ɓangare na tallafa wa gwamnatin jihar Kano, wajen yaƙi da ta'ammali da kayan maye.

A yayin taron, Jami'an hukumar NDLEA, reshen jihar Kano, sun nuna wa ɗalibai illar da kayan maye suke yi ga jikin ɗan adam a bayyane, musamman irin su Sholisho, Madarar Sukudayin da dai sauransu.

Da yake zantawa da Dala FM Kano, shugaban ƙungiyar matasan ƴan jarida ta jihar Kano, wato Kano Youth Journalist Forum, Kwamared Musa Zangina Adam, ya ce sun ɗauki gaɓarar wayar da kan ɗaliban makarantun sakandaren ne bayan da Ma'aikatar ilimi ta jihar ta sahale musu.

A cewar sa, kasancewar sun yi la'akari da cewa suma matasan ƴan jaridar akwai rawar da ya kamata su taka wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi, a don haka ne suka dukufa wajen wayar da kan matasan kan illar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

Kwamared Musa Zangina ya kuma ce, a yayin taron sun samu wakilci daga hukumar hana sha da dillancin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, tare da zuwan tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Ɗantiye, da wakilci daga ma'aikatar ilimi da sauran ɓangarori, inda suka faɗakar da ɗaliban kan illar shan kayan maye.

Da yake nasa jawabin a yayin taron, Tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Alhaji Baba Halilu Ɗantiye, buƙatar iyaye ya yi da su ƙara jajircewa wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, domin kaucewa faɗawar su cikin harkokin shaye-shaye.

Ƙungiyar matasan ƴan jaridar ta jihar Kano, ta kuma ce za ta kammala taron wayar da kan ɗaliban nan da makwanni uku masu zuwa, a sauran makarantun Sakandiren da suka rage guda uku.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM