Ɗan takarar Gwamnan Kano ya yi alƙawarin mafi ƙarancin albashin Naira miliyan ɗaya.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Ɗan takarar Gwamnan Kano a ƙarƙashin jam'iyyar APM mai alamar Rogo, Alhaji Muhammad Bashir Galadanchi, ya ce babban aikin da zai fara yi ga al'ummar jihar shi ne samar musu da mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu 500 zuwa miliyan Ɗaya.
Alhaji Muhammad Bashir Galadanchi ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a ranar Alhamis a shalkwatar jam'iyyar dake Dakata, ƙaramar hukumar Nassarawa.
Muhammad Bashir ya ƙara da cewa zai yi ƙoƙari wajen mayar da hankali kan yaƙi da cin hanci da samar da ayyukan yi sai kuma bayar da ilimi kyauta kuma wajibi tun daga matakin firamare da sakandare.



