Koma Labarai
Labarai

NDLEA, ta kama mutane 2, da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 499.3, ta ƙwato ƙwayoyin Tramadol 3,840 a Kaduna.

Hassan Mamuda Ya'u 1 views
NDLEA, ta kama mutane 2, da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 499.3, ta ƙwato ƙwayoyin Tramadol 3,840 a Kaduna.

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, ta kama mutane biyu tare da ƙwato tabar wiwi mai nauyin kilogiram 499.3 a yankin Gonin Gora na Jihar Kaduna.

Hukumar ta kuma ƙwato ƙwayoyin Tramadol guda 3,840 a wani samame na daban.

Jaridar Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami'in Yaɗa Labaran NDLEA a Kaduna, S. Garba ASN, ya fitar.

Ya ce, jami'an hukumar sun kai samame wata maboya a Gonin Gora ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026, inda suka kama Celestine Chime, mai shekara 34, da Chibueze Christ, mai shekara 36, tare da ƙwato tabar wiwi nau'in Skunk mai nauyin kilogiram 499.3.

Hukumar ta ce, a wani aikin daban da aka gudanar ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, jami'an NDLEA sun kama Samson Chibuike Andebe, mai shekara 30, a yankin Grace Land da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari.

NDLEA ta kuma kama ƙwayoyin Tramadol guda 3,840 masu ƙarfin 225mg, waɗanda nauyinsu ya kai kilogiram 2.5.

Shugaban NDLEA na Jihar Kaduna, CN Maijama'a, ya yaba wa jami'an hukumar kan ayyukan da suka gudanar, tare da bayyana alaƙar da ke tsakanin amfani da miyagun ƙwayoyi, fataucinsu da wasu nau'ikan laifuka.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM