Peter Obi ya nemi a gaggauta kama waɗanda suka kai wa ayarin motocin Kwankwaso hari a Bichi.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC Peter Obi, ya yi kira ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, da sauran hukumomin tsaro, da su binciki harin da aka kai wa ayarin motocin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, a ƙaramar Hukumar Bichi ta Jihar Kano, tare da gaggawar kama waɗanda ke da hannu.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan dai na cikin sanarwar da Peter Obi ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba, 2026.
Obi ya bayyana cewa rahotannin da ya samu sun nuna cewa, yayin harin wasu daga cikin mutanen da ke cikin ayarin Kwankwaso sun samu raunuka, yayin da aka lalata motoci kusan guda bakwai.
Ɗan takarar ya kuma yi Allah wadai da lamarin, tare da neman hukumomin tsaro su gano duk waɗanda suka aikata harin, domin gurfanar da su a gaban kotu.
Peter Obi, ya ce bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama dalilin tashin hankali ko lalata dukiyoyi ba, tare da yi wa waɗanda suka samu raunuka fatan samun sauƙi.



