Koma Labarai
Labarai

Gwamnan Kano ya sanar da sakin matarsa, tare da gayyatar mata masu sha’awar aurensa su nemi dama.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Kano  ya sanar da sakin matarsa, tare da gayyatar mata masu sha’awar aurensa su nemi dama.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar a bainar jama’a cewa ya amince da sakin matarsa ta biyu, Zainab Musa Kwankwaso, ’yar tsohon ubangidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga ’yan fansho a gidan gwamnatin Kano ranar Litinin 16 ga Nuwamba, 2026, inda ya yi amfani da kalaman sojojin baka wajen bayyana sauya matsayinsa daga mai mata biyu zuwa mai mata ɗaya.

Gwamnan ya ce ya amince da zama da mace ɗaya a yanzu, amma yana da niyyar sake yin aure.

Ya kuma ce ya umarci kwamishinan yaɗa labarai da ya sanya sanarwa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta, domin gayyatar matan da ke sha’awar neman aurensa.

Ya bayyana cewa yana farin ciki da matakin da ya ɗauka, tare da roƙon Allah Ya nisantar da shi daga mutanen banza, ya kuma haɗa shi da na gari.

A ranar Asabar ne Zainab ta shigar da ƙara a kotu tana neman saki a kotun Upper Area Court da ke Gudu, Abuja. Kotun ta umarci gwamnan da ya gurfana a gabanta ranar 17 ga Nuwamba, 2026.

An daura auren Zainab da gwamnan ne a ranar 29 ga Yuli, 2006, kuma sun haifi ’ya’ya shida tare da shi.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM