Koma Labarai
Labarai

Hisbah ta kama matasa uku kan zargin cin mutuncin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hisbah ta kama matasa uku kan zargin cin mutuncin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta kama matasa uku bisa zargin su da cin zarafin hukumar, da kuma babban Kwamandan ta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, a shafin Tiktok.

Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dr. Mujahedeen Aminuddeen Abubakar ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba, 2026.

Ya ce matasan da ake zargin sun haɗar da Ahmad Usman (Ortega) Mai shekaru 25, ɗan unguwar Kurna, da Muhammad Aliyu ɗan shekaru 20, mazaunin unguwar Kurna, sai Zainab Abubakar mai shekaru 19, ƴar asalin jihar Ogun, wadda ke zaune a unguwar Ɗorayi.

A cewar sa, ana zargin matasan da amfani da shafin su na Tiktok, wajen cin zarafin hukumar Hisbah, da Babban Kwamandan hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Dr. Mujahedeen ya kuma ƙara da cewa, yanzu haka hukumar na ci gaba da gudanar da bincike a kan matasan, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM