Koma Labarai
Labarai

Ba zan yi wa kowa kamfen ba, tunda ni ba ɗan siyasa ba ne - Sheikh Daurawa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ba zan yi wa kowa kamfen ba, tunda ni ba ɗan siyasa ba ne - Sheikh Daurawa

Fitaccen malamin addinin musulunci, kuma Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce ba zai yi wa kowa kamfen ba kasancewar shi ba ɗan siyasa ba ne.

Kalaman Daurawa na zuwa ne bayan da a makon da ya gabata Jam'iyyar APC ta saka sunansa cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa Tinubu da na gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Malamin ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce shi ba ɗan siyasa ba ne amma zai yi wa duk wanda zai wa al'umma adalci fatan nasara.

A cewar malamin, "amma ina fata duk wanda zai tabbatar da adalci, ya tausaya wa talakawa, ya kare haƙƙinsu Allah ya ba shi nasara".

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM