Ƴan bindiga sun kashe Sheikh Yahaya Masussuka a gidansa da ke jihar Katsina.

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke garin Dutsin-Ma, Jihar Katsina.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare, a ƙofar gidan malamin, lokacin da maharan suka buɗe masa wuta tare da wani amininsa.
Bayan harin, an garzaya da su zuwa Asibitin Dutsin-Ma domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu, kamar yadda kafar Premier Radio Kano ta ruwaito.
Har zuwa wannan lokaci, ba a samu cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka kashe malamin ba.
Kisan ya jefa al’ummar Dutsin-Ma cikin alhini, musamman mabiyan Sheikh Yahaya Masussuka da sauran waɗanda suka san shi.
Rahotanni sun bayyana cewa, al'umma sun yi dafifi a ƙofar gidan malamin a cikin daren wannan rana.



