Ya kamata a rinƙa baiwa matasa muƙamai don damawa da su a gwamnati - Comrd. Auwal Awareness

Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano, a jam'iyyar Youth Party, Kwamared Auwal Usman Awareness, ya ƙalubalanci yadda shugabanni ke wofantar da matasa wajen bada muƙamin siyasa, duk kuwa da irin rawar da suke takawa a Najeriya.
Kwamared Auwal Awareness ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da Dala FM a ranar Juma'a 23 ga watan Oktoba, 2026.
Ya ce akwai abin takaici kan yadda ake gaza baiwa matasa muƙaman siyasa a ƙasar, la'akari da yadda suka lura da cewa da zarar gwamnatin tarayya za ta bada wani muƙamin siyasa sai a nemi tsofaffi a basu, inda ake wofantar da matasa.
Kwamared Auwal Awareness ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su rinƙa zaƙulo matasa wajen basu muƙaman siyasa matuƙar sun cancanci hakan, domin ganin suna dogaro da kan su.
Ya kuma buƙaci matasa da su ƙara tashi tsaye wajen ganin ana damawa da su a harkokin gwamnati, domin goben su ta yi kyau.



