Koma Labarai
Labarai

Ya kamata gwamnatin tarayya ta daƙile shirin ƴan Hausa Zallah a Najeriya - Dr. Abdullahi Getso

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ya kamata gwamnatin tarayya ta daƙile shirin ƴan Hausa Zallah a Najeriya - Dr. Abdullahi Getso

Babban Limamin masallacin juma'a na Jami'ulrrahman da ke unguwar Kundila a Kano, Dr. Abdullahi Muhammad Getso, ya ce akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin da ya dace wajen daƙile ayyukan ƴan Hausa Zallah, domin gujewa haddasa fitina a Najeriya.

Dr. Abdullahi Muhammad Getso, ya bayyana hakan ne a yayin taron Makon Sheikh Usman Ɗan fodiyo, da Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta ƙasa (MSSN) reshen jihar Kano, ta gudanar ranar Talata 27 ga Oktoba, 2026, a ɗakin taro na Makarantar koyon harshen larabci ta SAS, da ke Kano.

Ya ce duba da yadda ƴan Hausa Zallan ke da wata mummunar aƙida da ka iya kawo husuma a ƙasar, akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin an daƙile mummunar manufar su.

A cewar sa, "Ƴan Hausa Zallan suna bayyana cewa wai duk ɗan Fulani ɗan ta'adda ne tun zamanin Shehu Usman Ɗan fodiyo, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne, domin Shehu Ɗan fodiyo, ya bada dukkan gudunmawar da ta dace ga addini da al'umma," in ji shi.

Dr. Getso ya ƙara da cewa, la'akari da illar da ƴan Hausa Zallan ke haifar wa a ƙasa, ya kamata hukumomin tsaro da gwamnati su ɗauki matakan daƙile shirin su, don wanzuwar zaman lafiya a Najeriya.

Da yake nasa jawabin, shugaban taron, kuma malami da ke koyarwa a jami'ar Bayero da ke nan Kano, Farfesa Muhammad Babangida Muhammad, ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kan matasa kan mahimmancin sanin tarihin magabata, irin su Shehu Usman Ɗan Fodio, da sauran su.

Mallam Babangida Sa'idu Aminu, shi ne shugaban Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta ƙasa MSSN, reshen jihar Kano, ya ce sun gayyaci ɗalibai daga makarantu daban-daban wajen halartar taron Makon Shehu Usman Ɗan fodiyo, domin sanar da tarihin sa don sanin irin gudunmawar da ya baiwa al'umma.

A yayin taron al'umma da dama ne suka samu damar halarta daga gurare daban-daban, inda aka gabatar da maƙaloli daban-daban da ka iya taiamak wa ɗalibai a harkar karatun su.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM