DA Ɗumi-Ɗumi: Gwamnan Kano ya cire Ibrahim Waiya daga Kwamishinan yaɗa labarai

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sauya wa wasu kwamishinoni ma'aikatun da suke jagoranta, tare da bayyana sabbin muƙaman kwamishinonin da ya naɗa.
Wannan na cikin jerin sunayen da Ibrahim Adam, hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kafafen sada zumunta, ne ya wallafa, na jerin sabbin ma'aikatun da kwamishinonin za su jagoranta.
A cikin sabon tsarin rabon ma'aikatun, an mayar da Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya zuwa Ma'aikatar Matasa da wasanni, yayin da Hon. Safiyanu Hamza Kachako aka mayar da shi Ma'aikatar Muhalli.
Sauran kwamishinonin da aka ware wa ma'aikatun sun haɗar da:
1. Hon. Yushau Soja – Ma'aikatar Tsaro da al'amuran cikin gida.
2. Hon. Idris Garba Mustapha – Ma'aikatar Ayyuka na Musamman.
3. Hon. Muntari Ishaq Yakasai – Ma'aikatar Jinƙai.
4. Hon. Ibrahim Namadi Dala – Ma'aikatar Kasuwanci.
5. Hon. Ibrahim Tsanyawa – Ma'aikatar Kimiyya da Fasaha.
6. Hon. Safiyanu Kachako – Ma'aikatar Muhalli.
7. Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya – Ma'aikatar Matasa.



