Majalisar dokokin Kano ta tsawaita wa’adin dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Rogo, Ɓagwai da Bebeji na tsawon watanni uku.

Majalisar dokokin jihar Kano ta ƙara wa’adin dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Rogo da Bagwai da kuma Bebeji na tsawon watanni uku.
Haka kuma, majalisar ta ƙara wa kwamitin wucin-gadi da ta kafa domin binciken zarge-zargen da ake yi wa shugabannin, wa’adin gudanar da bincikensa zuwa watanni uku.
A baya, majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakinta, Jibril Isma’il Falgore, ta dakatar da shugabannin uku sakamakon wasu ƙorafe-ƙorafe da suka shafi zargin karya ƙa’idojin gudanar da ayyuka da bin tsarin mulki.
Kakakin majalisar ya bai wa kwamitin watanni uku domin gudanar da cikakken bincike, tare da gabatar da rahotonsa ga majalisar.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sanusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, wannan na zuwa ne bayan ƙarewar wa’adin farko, inda majalisar ta amince da ƙara wa’adin dakatarwar shugabannin da na kwamitin da wasu watanni uku, domin ba shi damar kammala binciken ƙorafe-ƙorafen da gabatar da rahotonsa ga majalisar.



