Koma Labarai
Labarai

Iyaye ku tsawatar wa ƴaƴan ku illar shiga bangar siyasa - Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa

Hassan Mamuda Ya'u 9 views
Iyaye ku tsawatar wa ƴaƴan ku illar shiga bangar siyasa - Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa, ta buƙaci iyaye da su tsawatarwa ƴaƴansu kan kaucewa shiga bangar siyasa a tarukan yaƙin neman zaɓen 2026.

Shugaban Ƙungiyar Kwamared Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano, ranar Litinin 2 ga Nuwamba, 2026.

Ya ce duba da yadda a wasu lokutan wasu ƴan siyasa ke amfani da matasa wajen basu miyagun ƙwayoyi da makamai, wajen zuwa tarukan siyasa, akwai buƙatar iyaye su ƙara tsawatarwa da ƴaƴan su don kaucewa bari ayi amfani da su ta wannan fuskar.

Ya kuma ce akwai buƙatar duk ɗan siyasar da ya ce matasa su fito da makamai su je bangar siyasa, ko basu miyagun ƙwayoyi, to su faɗa masa ya fito da ƴaƴansa su fita tare.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM