Koma Labarai
Labarai

Hukumar KSCPC, ta ƙona kayayyakin da suka lalace da marasa ingancin da ta ƙwace a kasuwannin Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar KSCPC, ta ƙona kayayyakin da suka lalace da marasa ingancin da ta ƙwace a kasuwannin Kano.

Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara na musamman kan harkokin Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Jihar Kano (KSCPC), Hon. Hassan Muhammad Sagir, ya jagoranci aikin lalata kayayyakin da wa'adin amfaninsu ya ƙare, da kuma waɗanda ba su da inganci.

Hukumar dai ta ƙwace kayayyakin ne a yayin gudanar da ayyukan sa ido da tabbatar da bin doka a faɗin jihar.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan sashen wayar da kan jama'a na hukumar KSCPC, Jamilu Mustapha Yakasai ya fitar a ranar Talata 3 ga watan Nuwamba, 2026.

Sanarwar ta ce, da yake jawabi yayin gudanar da aikin, Hon. Sagir ya bayyana cewa, kayayyakin da aka lalata sun haɗar da waɗanda wa'adin amfaninsu ya ƙare, suka lalace ko kuma ba su dace da amfanin ɗan Adam ba.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kwashe kayayyakin tare da lalata su.

Ya kuma bayyana cewa mafi yawan kayayyakin da aka ƙwace an adana su ne a ma'ajiyar hukumar, inda taruwarsu da kuma warin da suke fitarwa za su iya haifar da matsalolin muhalli da barazana ga lafiyar ma'aikatan hukumar da mazauna yankunan da ke kusa da wurin.

Hon. Sagir ya yi kira ga 'yan kasuwa da masu harkokin kasuwanci da su ba hukumar haɗin kai wajen yaƙi da yaɗuwar kayayyakin da suka ƙare wa'adin amfani, waɗanda aka gurɓata da kuma marasa inganci a Jihar Kano.

Ya jaddada cewa hukumar, ƙarƙashin jagorancin Sakataren Zartarwarta, Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ba za ta lamunci duk wani nau'i na cutar da masu sayayya ko kuma harkokin kasuwanci da ke jefa lafiyar al'umma cikin haɗari ba, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka sun saɓa wa doka.

Hon. Hassan ya kuma nuna godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa dama da goyon bayan da ya ba shi na jagorantar wannan aikin lalata kayayyakin.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM