Gwamnan Kano ya tura sunan mai magana da yawun sa, Sanusi Bature majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar, domin tantancewa tare da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Hakazalika, Gwamnan ya miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani, da shima zai naɗa shi a matsayin Kwamishina.
Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 10:00 na safe.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Litinin, ya ce Majalisar ta karɓi wasiƙar buƙatar tantancewar ne daga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kamalu ya ƙara da cewa, za a gudanar da aikin tantancewar ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.
Sanarwar ta ce za a gudanar da aikin tantancewar ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore.
Sanusi Bature Dawakin Tofa dai shi ne mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, kuma yana cikin mutum biyu da gwamnan ya miƙa sunayensu domin zama kwamishinoni a gwamnatin jihar Kano.



