Gwamnatin Kano za ta ɗauki nauyin karatun mutanen da suka musulunta a faɗin jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ɗauki nauyin karatun dukkan mutanen da suka musulunta a Kwalejin Shari'a da Ilimin Addinin Musulunci ta Legal, ƙarƙashin Hukumar Shari’a ta Jihar Kano.
Gwamnatin ta ƙudiri wannan aniyar ne domin baiwa mutanen damar samun ilimin addinin Musulunci ba tare da fuskantar matsalar biyan kuɗin makaranta ba.
Shugaban Kwalejin Shari'a da Ilimin Addinin Musulunci ta jihar Kano, (Legal) Dakta Tamasi Ali Ma’az, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske kan shirye-shiryen kwalejin a ranar Litinin 14 ga watan Satumba, 2026.
Wannan na zuwa ne a wani ɓangare na ƙaddamar da Kalandar Musluncin da Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta ƙaddamar yau Litinin, a ɗakin taro na Coronation da ke gidan Gwamnatin jihar Kano.
Dr. Tamasi ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na tallafa wa sabbin musulunta wajen samun ingantaccen ilimin addinin Musulunci, domin su fahimci koyarwar addinin tare da sauƙaƙa musu damar gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar Musulunci.
A cewar sa, "Ɗaukar nauyin karatun zai taimaka wajen rage musu nauyin kuɗaɗen karatu, musamman ganin cewa wasu daga cikinsu na iya kasancewa ba su da isassun hanyoyin samun kuɗin biyan makaranta," in ji Tamasi.
Ya kuma ƙara da cewa, shirin zai ba sabbin tuba damar samun ilimi cikin sauƙi, tare da ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da karatunsu, da fahimtar addinin Musulunci yadda ya kamata.



