Koma Labarai
Ilimi

Hukumar Shari'a ta Kano ta ƙaddamar da kalandar Muslunci ta 1448 bayan Hijira.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Shari'a ta Kano ta ƙaddamar da kalandar Muslunci ta 1448 bayan Hijira.

Hukumar Shari'a ta jihar, ta Ƙaddamar da Kalandar Muslunci ta shekarar 1448, guda 30,000, domin amfanar da al'umma a faɗin jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Hukumar ta ƙaddamar da Kalandar ne a ɗakin taro na Coronation da ke gidan Gwamnatin jihar Kano, ranar Litinin 14 ga watan Satumba, 2026.

Da yake jawabi, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya ce an ƙaddamar da Kalandar Musluncin ne domin amfanar da al'ummar musulmi a jihar, da ƙasa, da ma duniya baki ɗaya.

Sheikh Ali Ɗan Abba ya kuma jaddada buƙatar Shugaban Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ga wakilan da aka baiwa Kalandar da su isar da ita zuwa ga waɗanda suka dace ba tare da sun karɓi kuɗin kowa ba.

A cewar sa, "Gwamnatin jihar Kano ce ta buga Kalandar har guda dubu Talatin (30,000) domin a raba su kyauta ga al'umma, domin a amfanar da al'umma ilimin addinin musulunci," In ji shi.

A nasa ɓangaren, Shugaban Ma'aikatan fadar gwamnatin Kano, Dr. Sulaiman Wali Sani, kuma wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin taron, ya yabawa hukumar shari'ar bisa ƙoƙarin da take yi wajen ciyar da addinin musulunci, da ma al'umma gaba.

Ya kuma buƙaci al'umma musamman ma waɗanda suka samu kalandar da su yi amfani da ita ta yadda ya dace, domin sanin ranaku da watannin musulunci, da ma amfana da ilimin da ke cikin kalandar.

Jim kaɗan da ƙaddamar da kalandar, an rarraba ta ga wakilai daga ɓangarorin Gwamnatin Kano, da Ƙananan hukumomi, ma'aikatu, da hukumomi, da kuma hukumomin tsaro, da sauransu.

Taron ya samu halartar al'umma da dama, ciki har da wakilci daga gwamnatin Kano, Masarautar Kano, hukumomin tsaro, Limamai, Malamai, Ƙungiyoyi, da dai sauransu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM