Gwamnatin Kano ta naɗa Kwamishinan shari'a Maude SAN, don ya shugabanci kwamitin inganta tsarin almajirci a jihar

Gwamnatin Kano ta naɗa Kwamishinan Shari'a na jihar a matsayin shugaban kwamitin inganta tsangayu, domin kyautata makomar al'majirai da samun ilimi mai inganci a faɗin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Umar Farouk, ne ya ƙaddamar da kwamitin a ofishin sa da yammacin ranar Laraba 2 ga Satumba, 2026.
Alhaji Umar Farouk ya ce, manufofin kwamitin shi ne a inganta tsangayu domin samun ingantaccen ilimin Al-kur'ani mai girma.
An kuma ɗorawa kwamitin alhakin kawo inganci da kyautata makomar Almajirai da kuma lura da hakkokin su wanda dokar ƙasa ta basu.
Da yake bayani a wajen ƙaddamarwa da kwamitin, Kwamishinan Shari'a na jihar Kano, Barrister Abdulkarim Maude SAN, ya godewa gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa yadda ya samu ƙwarin gwiwa a kan sa har aka dora masa wannan nauyi.
Barrister Maude, ya kuma bayyana cewar zai yi aiki da sauran yan kwamitin domin ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa, ragowar yan kwamitin sun haɗar da kwamishinonin ilimi Dr. Gwani Ali Haruna Makoɗa, da na yaɗa labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, da kuma wasu shugabannin hukumomi da ke jihar Kano.


