Koma Labarai
Addini

Ku fara duban jinjirin watan Shawwal daga gobe Laraba - Sarkin Musulmi

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ku fara duban jinjirin watan Shawwal daga gobe Laraba - Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Laraba, 29 ga watan Ramadan 1447, wanda ya yi daidai da 18 ga watan Maris, 2026.

Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 17 ga watan Maris, 2026.

Sanarwar ta kuma buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi.

Kazalika, Wazirin Sakkwato, ya kuma yi addu’a Allah Ya taimaka musu a wannan muhimmin aikin na addini da su ke yi.

Masarautar ta kuma ce idan har ba a ga watan na Shawwala a ranar Laraba ba, hakan na nufin za a yi sallah ƙarama a ranar juma’a, akasin haka kuma za a yi sallah a ranar Alhamis.

Ready to PlayDala FM88.5 FM