Koma Labarai
Lafiya

Tinubu ya amince da ware Naira Biliyan 10 don shirin gaggawa na daƙile cutar Ebola a Najeriya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tinubu ya amince da ware Naira Biliyan 10 don shirin gaggawa na daƙile cutar Ebola a Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kashe Naira biliyan 10 domin ƙarfafa shirye-shiryen gaggawa na dakile yiwuwar bullar cutar Ebola a ƙasar, bayan rahotannin sake ɓarkewar cutar a wasu ƙasashen Afirka.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata 9 ga Yuni, 2026.

A cewar sa "Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma amince da kafa Kwamitin gaggawa na Fadar Shugaban Ƙasa, domin sa ido da daidaita shirye-shiryen tunkarar Ebola da sauran barazanar lafiyar jama'a, in ji shi.”

Sanarwar ta ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen ƙarfafa ayyukan Hukumar Dakile Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), da kuma tallafa wa sauran shirye-shiryen kariya na gaggawa, musamman bayan sake bullar cutar a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Uganda.

Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, tare da wakilai daga ma’aikatu, hukumomi da gwamnatocin jihohi.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci hukumomin da abin ya shafa da su tsaurara bincike a kan matafiya a filayen jiragen sama da sauran mashigai, tare da ɗaukar matakan kariya domin hana shigowar cutar Ebola cikin Ƙasar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM