Koma Labarai
Lafiya

Gwamna Abba Kabir ya taya Sarkin Kano Sanusi II murnar cika shekaru 65 da haihuwa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamna Abba Kabir ya taya Sarkin Kano Sanusi II murnar cika shekaru 65 da haihuwa

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya taya Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, murnar cika shekaru 65 da haihuwa.

Wannan na cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a 31 ga Yuli, 2026.

Gwamnan ya bayyana Sarkin a matsayin jagora mai hangen nesa, da hikima, da kuma jarumtaka da kishin tabbatar da adalci.

Abba Yusuf ya kuma yaba da irin gudunmawar da Sarkin ya bayar wajen gina kasa, bunkasa ilimi da tattalin arziki, da kuma kare al’adu da addinin Kano.

Ya kuma ce tsawon shekarun da Sarkin ya yi yana hidima ga al’umma sun sanya ya samu karbuwa a ƙasar nan, da kuma ƙasashen duniya.

Gwamnan ya kuma yaba da ƙoƙarin Sarkin wajen inganta zaman lafiya, da hadin kai da shugabanci nagari, tare da bayar da muhimmanci ga ilimi, da tallafa wa mata da matasa, da kuma ci gaba mai ɗorewa da sauye-sauyen tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa jagorancin Sarkin ya kasance abin koyi da kuma hasken fata da ci gaba ga al’ummar Kano da sauran sassan kasa.

Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya bai wa Sarkin lafiya, da tsawon rai da ƙarin hikima domin ci gaba da jagorantar Masarautar Kano, da bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

Har ila yau, gwamnan ya sake tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da masarautar gargajiya wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma da kuma ƙara ɗaukaka matsayin Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM